Jam’iyyar APC ta maganta akan zaben Abuja a karamar hukumar Gwagwalada — Nigeria Today
Pages Navigation Menu

Latest and breaking news, sports and all that is trending today

Jam’iyyar APC ta maganta akan zaben Abuja a karamar hukumar Gwagwalada

– Wata jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana tunaninta akan zaben Abuja wanda an yi a karshen mako da ya wuce

– An rahoto wanda Jam’iyyar APC ta da dan Majalisa mai suna Zakari Angulu Dobi suke maganta

Wani dan jarida mai suna Sani Musa daga Abuja ta ruwaito wanda, jam’iyyar APC na gundumar Dobi dake karamar Hukumar Gwagwalada dake birnin tarayya Abuja ta bayar da sanarwar dakatar da dan majalisar wakilai na mazabar Abuja ta Kudu, Alhaji Zakari Angulu Dobi daga jamiyar.

KU KARANTA KUMA:

Da yake yi wa mafarauta labarai jawabi a ofishin jam’yiyar na gundumar Dobi mataimakin shugaban jam’iyyar na Dobi, Mallam Ciroma Zagi ya ce manyan shugabanin jam’iyyar sun yanke shawarar dakatar da Alhaji Zakari Angulu ne saboda zagon kasa da yake yi mata.
zaben abuja

Tutar jam’iyyar APC

Ciroma Zagi ya ce dan majalisar bai yi wa dan takarar jam’iyyar na shugabancin karamar hukumar Gwagwalada na APC Alhaji Abubakar Jibrin Giri kamfen ba, ya ce ya yi wa dan APGA ne kamfen.

Sannan ya kuma zargi Zakari Angulu Dobi da shirya rigima tare da tayar da zaune tsaye a lokacin zaben a garin sa na Dobi. Inda ‘yan bangar siyasa suka kashe wani mai gadi tare da lalata kayayyakin wasu daga cikin jigogin jam’iyyar APC na yankin.

Da yake mayar da martani, Dan majalisa Zakari Angulu Dobi ya ce mataimakin shugaban jam’iyyar na gundumar Dobi ba shi da hurumin dakatar da shi, ya ce akwai ka’idoji da jam’iyyar ta shimfida wajen daukar irin wannan mataki.

Inda ya e Ciroma Zagi ya shirya domin kare kansa dangane da wadannan zarge- zarge da ya yi masa a gaban kotu.

The post Jam’iyyar APC ta maganta akan zaben Abuja a karamar hukumar Gwagwalada appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

Do you have something awesome to share with the world? Click here to share

Do you ever have any question about anything you wish to ask and get answer? Click here to ask

Follow us on twitter @NigeriaTodayNG

Also, Like us on facebook

This post was syndicated from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM. Click here to read the full text on the original website.

Comments

Be the First to Comment!

avatar
  Subscribe  
Notify of
Download the Nigeria Today app from Play store. Click here download now
Hello. Add your message here.