Yan majalisar tarayya sun zaftare Naira Biliyan 17 daga kasafin kudin 2016 — Nigeria Today
Pages Navigation Menu

Latest and breaking news, sports and all that is trending today

Yan majalisar tarayya sun zaftare Naira Biliyan 17 daga kasafin kudin 2016

– Majalisar dattawan Najeriya sun gana kan kasafin kudin Najeriya na 2016

– Yan majalisar kuma sun amince da kasafin kudin 2016 a Laraba 23, ga watan Maris

Rahotanni na cewa daga jaridar Rariya wanda, majalisun dokokin tarayya sun zaftare Naira Biliyan 17 daga ciki kasafin kudin Bana bayan da majalisar dokokin tarayya suka gabatar da kasafin kudin bana a jiya, bincike ya nuna cewa an zaftare adadin kudi naira biliyan goma sha bakwai da wasu ‘yan kai.

KU KARANTA KUMA:

Yayin da da yake bayyana amincewar majalisun kan kasafin kudin, shugaban majalisar dattijan, Sanata Bukola Saraki ya yi wa bangaren zartaswa gargadi, cewa ya tabbatar ya yi amfani da kudaden yadda ya dace ba tare da kauce hanya ba. Honarebul Kawu Smaila mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin majalisa yace yana zaton cewa abun da majalisun suka yi zasu samu yadda dashi domin sun samu fahimta ta aiki tare da majalisun.

naira biliyan 17

Shugaban majalisar dattawan Najeriya , Bukola SARAKI

Wani abun da ya dauki hankalin jama’a shi ne yadda majalisun suka rage kasafin da kashi goma cikin dari.

Sanata Muhammad Danjuma Goje shugaban kwamitin dake kula da kasafin kudi yace dole ne su yi abun da zai yiwu ba abun da ba zai yiwu ba. Yace tunda aka fara mulkin dimokradiya ba’a taba rage kasafin kudi ba saidai a kara da zara shugaban kasa ya gabatar dashi. Da ‘yan majalisa karawa suke yi amma a wannan karon sun rage. Dalilin ragewa kuma shi ne wahalolin da ake ciki da kuma faduwar farashen man fetur. Abun da suka yi taimakon shugaban kasa ne suka yi.

A bangaren majalisar wakilai Ahmed Babba Kaita ya ce kasafin ya sake wa Najeriya lale. Kasafin kudin bana ko ina mutum yake a kasar ya taba shi. Kasafin ya kuma sauya makomar kasar domin ya sa hankali akan maganar noma da ma’adanai.

The post Yan majalisar tarayya sun zaftare Naira Biliyan 17 daga kasafin kudin 2016 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

Do you have something awesome to share with the world? Click here to share

Do you ever have any question about anything you wish to ask and get answer? Click here to ask

Follow us on twitter @NigeriaTodayNG

Also, Like us on facebook

This post was syndicated from Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM. Click here to read the full text on the original website.

Comments

Be the First to Comment!

avatar
  Subscribe  
Notify of
Download the Nigeria Today app from Play store. Click here download now
Hello. Add your message here.